Isa ga babban shafi
Nijar

A kalla dala miliyan 128 aka sace a Gwamnatin Tandja

A kalla kudi CFA biliyan 64 ne dai dai da dalar Amurka 128 aka sace daga asusun gwamnatin Nijar a zamanin gwamnatin Tsohon shugaban kasa Mamadou Tandja, kamar yadda wani Jami’in ofishin binciken kudin kasar ya sanar.Tuni dai gwamnatin sojin kasar ta kaddamar da sabon binciken gwamnatin tsohon shugaban bayan hambarar da shi a watan Fabrairu tare da kargame shi a kurkuku.A cewar Gabriel Martin, al’amurran da suka shafi sama da fadi da kudaden jama’a da dama ne aka gano wadanda suka hada da kwangilolin jabu, inda kuma aka gano mutane sama da 2,000 na da hannu a ciki dumu-dumu hadi da tsohon shugaba Mamadou Tandja.Kasar Jamhuriyyar Nijar wacce ke samar da makamashin Uranium ga kasar Faransa, na daya daga cikin kasashen Africa masu fama da matsanancin talauci inda akasarin al’ummar kasar ke zama kasa da dala daya a rana. 

Mamadou Tandja tsohon shugaban kasar Jamhuriyyar Nijar.
Mamadou Tandja tsohon shugaban kasar Jamhuriyyar Nijar. AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.