Isa ga babban shafi
Nijar

An amince da ‘yan takara 10 a zaben Shugaban kasar Nijar

Bayan tantance ‘yan takarar Shugabancin kasar Jamhuriyar Nijar, Bangaren shari’ar kasar ya amince da sunayen ‘yan takara goma da zasu kara a zaben kasar da za’a gudanar 31 ga watan Janairun badi.Zaben wanda za’a gudanar a kasar shi zai mayar da kasar zuwa mulkin demokradiyya bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Mamadou Tandja wanda ya fuskanci kalubale bayan ya yi fatali da kundin tsarin mulkin kasar don yunkurin tazarce.Daga cikin ‘yan takarar sun hada da Mahamadou Issoufou na Jam’iyyar PNDS wacce ta yi adawa da Shugaba Tandja sai kuma Mahamane Ousmane na Jam’iyyar CDS sai kuma tsohon Prime Minista Hama Amadou na Jam’iyyar MDN.Akwai kuma Bayard Mariama Gamatie mace ta farko a tarihin kasar wacce ta fito neman kujerar shugaban kasar a zaben da za’a gudanar.A karshen watan Janairu ne gwamnatin Sojin kasar karkashin jagorancin Janar Salou Djibo ta shirya gudanar da zaben. 

'yan takarar kujerar Shugabancin kasar Jamhuriyar Nijar.
'yan takarar kujerar Shugabancin kasar Jamhuriyar Nijar. RFI Hausa
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.