Isa ga babban shafi
Amurka

Attajirin Amurka ya kashe kansa a gidan yari

Attajirin Amurkan nan, Jeffery Epstein ya kashe kansa a gidan yari a daidai lokacin da yake dakon a yanke masa hukunci dangane da zargin sa da safarar kananan yara mata domin lalata da su.

Jeffrey Epstein
Jeffrey Epstein New York State Division of Criminal Justice Services/Handout/Fil
Talla

Epstein mai shekaru 66 wanda kuma ke da alaka da ‘yan siyasa da fitattun mutane a Amurka, ya rataye kansa ne a gidan yarin gyara halinka da ke birnin New York, yayinda aka tsinci gawarsa a safiyar yau Asabar.

A can baya dai, Epstein ya yi kokarin kashe kansa a wannan gidan yari, inda har ya yi wa kansa rauni a wuya.

Gabanin kashe kansa, Epstein na fuskantar barazanar daurin shekaru 45 muddin aka same shi da laifi, yayinda gwamnatin Amurka ta kaddamar da bincike kan mutuwarsa.

Marigayin ya musanta zargin da ake yi masa na sarafarar 'yan mata 'yan kasa da shekaru 18 domin karuwanci a kasaitattun gidajensa da ke Manhattan da Florida a shekarar 2002 da 2005.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.