A yau ne kasar Israela ke shagulgulan cika shekaru 70 da kafuwa, bayan mamaye kasar Falestinu da ta yi a gabas ta tsakiya, mamayen da ya haifar da tashe tashen hankulan da ke ci gaba da haifar da asarar rayukan falastinawan ta harsasan sojin mamayen yahudawa, sakamakon nuna tirjiya da Falestinawan ke ci gaba da yi.To don jin dalilan da suka haifar da kafa kasar, da kuma abubuwan da suka biyo bayan mamayen, Mahaman Salisu Hamisu ya tattauana da Dr Tukur Abdulkadir na jamíar Kaduna a Najeriya ga kuma yadda tattaunawarsu ta kasance.
Sauran kashi-kashi
-
Kwamandan MNJTF Janar Ibrahim Sallau kan nasarar su a yankin tafkin Chadi
Rundunar hadin gwuiwa da ke yaƙi da mayakan Boko Haram a Tafkin Chadi da ake kira MNJTF ta sanar da kashe mayaka 299 a cikin watanni 10 da suka gabata da kuma samun wasu 273 da suka mika kansu cikin lumana. Kwamandan rundunar Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali ya bayyana haka ga Babban Editan sashin Hausa Bashir Ibrahim Idris a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho bayan ya kwashe watanni 10 yana jagorancin rundunar mai cibiya a kasar Chadi.Ku latsa alamar sauti domin sauraren zantawar su.09/05/202406:33 -
Farfesa Dicko Abdurrahmae kan zaben Chadi
Yau Litinin aka bude rumfunan zabe a kasar Chadi, don zaben shugaban kasa da zai kafa sabuwar gwamnatin Chadi da ta kasance karkashin mulkin soji na tsahon shekaru 3.06/05/202403:30 -
Farfesa Umar Pate: Kan Ranar 'Yancin 'Yan Jarida ta Duniya
Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar ‘yan jaridu ta duniya, inda ake nazari a kan kalubalen da ma’aikatan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin inganta aikin.03/05/202403:41 -
Farfesa Kelani kan zargin da NNPCL ta yi wa wasu dillalan mai a Najeriya
Kamfanin man NNPCL ya ce yana da wadataccen man da za'a kwashe sama da wata guda ana amfani da shi a cikin gida, yayin da ya zargi wasu gurɓatattun dilallai da jefa jama'ar ƙasar cikin halin ƙunci.02/05/202403:06 -
Nuhu Abayo Toro: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya
Yau ce ranar Ma’aikata ta Duniya, kuma bikin na wannan shekara na zuwa ne a cikin mawuyacin hali ga ma’aikatan Najeriya, sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar da kuma kuncin rayuwar da suka samu Kansu.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro, Sakatare Janar na kungiyar kwadago ta kasa ta TUC.01/05/202403:23