Bakonmu a Yau
Amb. Kwande kan ganawar Buhari da Firaministar Birtaniya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:39
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar matsalar tsaro da kuma tattalin arziki ne suka fi damun sa a maimakon zaben shekara mai zuwa. Yayin ganawarsa da Firaministar Birtaniya, shugaban ya bayyana ma ta alkawura uku da ya yi wa 'Yan Najeriya lokacin zabe sune samar da tsaro da farfado da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa, kuma ana samun nasara kan wadannan alkawura. Sai dai Amb.Yahya Kwande, Dan kwamitin amintantu a Jam’iyyar APC, ya ce yana da shakku kan takarar Buhari kamar yadda za ku ji a hirarsa da Tasiu Zakari.