Isa ga babban shafi

Saudiya ta yi barazanar kai wa Qatar farmakin soji

Gwamnatin Saudiya ta yi barazanar daukar matakin soji akan kasar Qatar, muddin ta sayi makamin kakkabo jiragen yaki ko makami linzami kirar S-400 daga Rasha.

Makamin da ake amfani da shi wajen harbo jiragen yaki ko makamai masu linzami na Rasha, kirar S-400.
Makamin da ake amfani da shi wajen harbo jiragen yaki ko makamai masu linzami na Rasha, kirar S-400. Paul Gypteau / AFP
Talla

Jaridar Le Monde da ake wallafawa a Faransa ta rawaito cewa, cikin wasikar da ya aikewa shugaban Faransa Emmanuel Macron, Sarkin Saudiya Salman, ya nuna damuwa matuka akan tattaunawar da ake tsakanin Qatar da Rasha dangane da cinikin makamin na S-400.

Sarkin na Saudiya ya mallakar makamin kakkabo jiragen yakin ko makamai masu linzami ga Qatar, barazana ce ga tsaron Saudiya, don haka yake bukatar Faransa ta shiga tsakani.

A ranar 5 ga watan Yuni na shekarar 2017, Saudiya ta jagoranci kasashen Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Masar, wajen katse alakar diflomasiyya da Qatar, da kuma rufe kan iyakokinsu da ita na sama, ruwa da na kasa, bisa zargin kasar ta marawa ta’addanci baya.

Sai dai daga bisani Saudiyan ta gindayawa Qatar sharuddan sasantawa da suka hada da rufe sansanin sojin da Turkiya ta bude a kasar ta Qatar, da kuma rufe kafar yada labarai ta Aljazeerah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.