Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiya da Qatar ba su shirya sasantawa ba- Kuwait

Sarkin Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah wanda ke shiga tsakanin kan rikicin kasashen Saudi Arabia da Qatar ya ce har yanzu babu alamun kawo karshen rikicin ganin yadda bangarorin biyu ke nuna halin ko in kula akan sabanin da ke tsakaninsu.

Sarkin Kuwait Sheikh Sabah Al Khaled Al Sabah
Sarkin Kuwait Sheikh Sabah Al Khaled Al Sabah REUTERS/Hamad I Mohammed
Talla

A jawabi da ya gabatar ga Majalisar kasar a yau, Sheikh Al Sabah ya bayyana fargaba kan yadda har yanzu aka gaza magance rikicin wanda ya shiga watanni 5 da farawa, yana mai cewa babban muradinsa a yanzu bai wuce ganin an ceto kungiyar kasashen Yankin Tekun Fasha da ke neman durkushewa ba.

Ko a ziyarar da Sakataren harkokin Amurka Rex Tillerson ya kai wasu daga cikin kasashen yankin Gulf cikin karshen makon da ya gabata, ya shaida cewa Saudi Arabia ba ta shirya kawo karshen rikicin da ke tsakaninta da Qatar ba.

A cewar Saudiyya, Qatar ta gaza yin biyayya ga sharuddan da ta gindaya ma ta kafin ta amince su tattauna da juna don kawo karshen rikicin.

Sai dai kuma a bangare guda Qatar ta sanar da cewa a shirye ta ke ta tattauna da Saudiyya don kawo karshen rikicin amma ba tare da gindaya mata wasu harudda ba.

Sheikh Al Sabah ya ce za su ci gaba da bin matakan lalama don ganin an samu fahimtar juna tsakanin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.