Isa ga babban shafi
Afghanistan

IS ta kashe mutane sama da 50 a Kabul

Fiye da mutane 50 ne suka mutu yayinda wasu daruruwa kuma suka jikkata a wani harin da mayakan IS suka kai kan masallacin Shi’a a Kabul babban birnin Afghanistan.

IS ta kashe mutane a wani harin da ta kai birnin Kabul
IS ta kashe mutane a wani harin da ta kai birnin Kabul REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Wannan shi ne hari na uku a jere da kungiyar ke kai wa cikin wannan watan a birnin, galibi kan mabiyan darikar Shi’a.

Harin ya auku ne, a dai-dai lokacin da dubban al’umma ke gudanar da bikin cika shekaru 38 da mamayar da tarayyar Soveit ta yi wa Afghanistan a wata cibiyar al’adu a yammacin birnin, inda nan ne ake da wata ofishin wata jarida mai yaki da ayyukan ta’addancin kungiyar IS da ake kira Afghan Voice Agency.

Mai Magana da yawun ma’aikatar lafiya na Afghanistan Waheed Majroh ya shaidawa manema labarai cewa kawo yanzu akwai gawar mutane sama da 50 yayinda kuma wasu 84 ke karbar kulawar gaggawa.

Wani ma’aikaci a kafar yada labaran wanda ke wurin lokacin da aka kai harin, ya ce cikin wadanda harin ya rutsa da su akwai da dama daga cikin ma’aikatansu.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Nasrat Rahimi ya ce wanann shi ne mafi munin hari, tun bayan na watan Oktoba da ya hallaka mutum 50 a wurin bauta, aka kuma kara sanya wasu bama-baman biyu a dai-dai lokacin da ake shirin kwashe matattu da wadanda suka jikkata a harin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.