Isa ga babban shafi
Iraqi

Kurdawa na kada kuri'u a rumfunan zabe 2,065

Shugaban Kurdawan kasar Iraqi Massoud Barzani ya bijirewa duk wasu kiraye kirayen kasashen duniya na dakatar da kuri’a raba gardamar da aka shirya yi yau, inda yake cewa hadin kai da gwamnatin Iraqi ya kasa cimma biyan bukatar da suke nema.

Jami'an tsaro a daya daga cikin rumfunan zabe a garin Erbil yayin da suke duba masu kada kuri'a fin wucewa.
Jami'an tsaro a daya daga cikin rumfunan zabe a garin Erbil yayin da suke duba masu kada kuri'a fin wucewa. REUTERS/Ahmed Jadallah
Talla

Da safiyar yau Litinin, aka bude rumfunan kada kuri’u 2,065 da zasu shafe awanni 10 a bude, a birnin Erbil da ke arewacin Iraqi, babban birnin kasar Bagadaza, da kuma lardin Kirkuk mai arzikin man fetur.

Ana kuma sa ran akalla Kurdawa miliyan 5 da dubu 600 su kada kuri’unsu a zaben raba gardamar neman ballewar yankinsu daga Iraqi.

Gwamnatin Iraqi karkashin jagorancin Fira Minista Haider al Abadi ta sha alwashin kare hadin kan kasar a matsayinta na dukalalliya.

Tuni dai Fira minista al Abadi ya bukaci kasashen duniya da su daina sayen danyen man da ake hakowa a yankin na Kurdawa domin tilasta musu janye aniyarsu ta ballewa daga Iraqi.

Sai dai shugaban yankin Kurdawan Masoud Barzani, yace zaben ba wai zai shata iyakokin yankin bane, sai dai zai bada damar fara tattuanawa da gwamnatin Bagadaza wanda zai dauki shekara guda zuwa biyu kafin ballewar su daga Yankin.

Kasashen duniya da dama, musamman Turkiya da kungiyar kasashen Turai da Majalisar Dinkin Duniya duk sun bayyana adawa da zabe raba gardamar.

Ana ta matakin kasar Iran ta dakatar da sufurin jiragen samanta uwa yankin na Kurdawa, kamar yadda gwamnatin Iraqi ta bukata, yayinda kuma Turkiya ta yi gargadin cewa zata iya kakabawa yankin takunkumin karya tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.