Isa ga babban shafi
Turkiya

Kada kuri’ar ballewar yankin Kurdawa a Iraqi barazana ce - Turkiya

Fira ministan Turkiya Binali Yildrim, ya ce shirin kada kuri’ar raba gardama kan bukatar ballewar yankin Kurdawa a arewacin kasar Iraqi, barazana ce ga tsaronsu dan haka Turkiya zata dauki dukkanin matakan da suka dace na kariya.

Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan. Murat Cetinmuhurdar/Presidential Palace/Handout via REUTERS
Talla

A ranar Juma’ar da ta gabata, shugaban yankin Kurdawa da ke Iraqi, Mass’oud Barzani ya ce ba zasu jinkirta kada kuri’ar raba gardamar ba, duk da kiraye-kirayen jinkirtawar daga Amurka da sauran kasashen turai, bisa hujjar cewa matakin zai iya raunana kokarin da ake na murkushe mayakan ISIS a yankin gabas ta tsakiya.

Jim kadan bayan sanarwar ta Barzani, shugaban Turkiya Racep Tayyib Erdogan, ya ce matakin kin jinkirta kada kuri’ar ba karamin kuskure bane da shugaban yankin Kurdawan ya tafka, wato Barzani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.