Isa ga babban shafi
Syria

An bawa 'yan tawaye da fararen hula damar ficewa daga Daraya

‘Yan tawaye da fararen hula sun fara ficewa daga garin Daraya na kasar Syria, bayan da sojojin gwamnati suka kawo karshen kawanyar da suka yi wa birnin tsawon shekaru hudu da suka gabata.

Manyan motoci dauke da jama'ar da ke ficewa daga birnin Daraya
Manyan motoci dauke da jama'ar da ke ficewa daga birnin Daraya REUTERS/Omar Sanadiki
Talla

Daruruwan mutanen dai sun samu ficewa daga birnin na Daraya wanda ya kasance a cikin yankunan da suka fara tayar da boren nuna adawa da shugaba Bashar Assad a shekara ta 2011.

Mafi yawa daga cikin wadanda aka bawa damar ficewa daga birnin ‘yan tawaye ne da kuma iyalansu, inda aka rika saka su cikin motocin safa tare da rakiyar jami’an kungiyar Red crescent, daya daga cikin kungiyoyin agaji da ke kasar.

Motar farko na dauke ne tsofaffi, mata da kuma yara kanana, wadanda kusan dukkaninsu suna cikin hali na galabaita, yayin da a gefe daya dakarun gwmanatin Assad dauke da manyan makamai, ke sa-ido akan masu ficewa daga birnin.

Gwmanatin Syria dai ta kawo karshen killacewar da ta yi wa wannan gari, a daidai lokacin da sakataren wajen Amurka John Kerry, da ministar harkokin wajen Rasha Sergie Lavrov, da kuma manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Syria Stafan De Mistura, suka fara wani taro kan rikicin a birnin Geneva.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.