Isa ga babban shafi
Amurka-Syria-Rasha-Faransa

Amurka da Faransa sun zargi Assad da yin kafar angulu a zaman Sulhun Syria

Kasashen Amurka da Faransa sun zargi Gwamnatin Bashar al-Assad na Syria da yin kafar angulu a tattaunawar kawo karshan rikicin kasar da aka dakatar.

Jakadan Majalisar dinkin duniya na Musamman a Syria Staffan de Mistura
Jakadan Majalisar dinkin duniya na Musamman a Syria Staffan de Mistura REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya tuhumi Damascus da Rasha da yin kafar angulu ga kokarin dawo da zaman lafiya a Syria, bayan kaddamar da sabbin hare-hare a Yankin Aleppo.

Fabius ya ce ya zama wajibi kasashen duniya sun kira taro kan wannan al’amari domin ko shaka babu dage wannan tattaunawar na da nasaba da harin Rasha da kuma katse shigar da kayan jin kai zuwa wasu yankunan da gwamnati Syria ta yi da taimakon Rashan.

Ana sa bangaren sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, yace sabbin hare-haren Rasha da dakarun gwamnatin Syria a yankunan da ‘yan adawa ke rike dasu ya nuna kararra cewa ba a shirya rugumar manufar wannan zaman na samar da sulhu ga rikicin siyasar kasar ba.

A jiya laraba ne dai Jakadan Majalisar dinkin duniya na Musamman a Syria Staffan de Mistura ya sanar da dakatar da tattaunawar da ake gudanarwa a Geneva zuwa 25 ga watan Fabairu.

Sai dai a cewar sa hakan ba yana nufin wai an gaza cimma matsaya ba ne.

Dakatar da wannan tattaunawar na zuwa ne, kwana guda saura masu bada agaji su hallara birnin London domin tarar tallafin dala biliyan 9 ga Syria tare da cimma matsaya kan taimakawa miliyoyin al’ummar kasar dake hijira a kasashen dake makwabtaka da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.