Wani jami’in tsaron sa kai da aka bayyana sunansa da Bunu Bukar, ya tabbatar da misalign karfe 10 na safe lokacin da al’umma ke dawowa daga kauyen Goni Abachari zuwa Badu Kuluwa ne kwatsam mayakan na Boko haram akan babura suka bude wuta kansu tare da hallaka mutane 65.
A cewar mahukuntan yankin adadin mutanen da Boko Haram ta hallaka a harin ka iya karuwa bayan raunatar mutane da dama.