Isa ga babban shafi
Afrika

Mutane miliyan 600 na amfani da hasken rana don samun lantarki

Fiye da mutane miliyan 600 da ke fama da karancin wutar lantarki a yankin saharar Afrika yanzu haka sun rungumi sabuwar fasahar amfani da hasken rana wajen samar da lantarkin, sai dai duk da haka yankin na da karancin kwararru masu sarrafa sabuwar Fasahar.

Rahoton ya bayyana cewa yanzu haka yankin saharar Afrikan na da masana ko kuma kwararru a fannin samar da lantarkin ta hanyar hasken rana kasa da sufuri da adadin mutane dubu 16 kacal da ke aiki a sashen
Rahoton ya bayyana cewa yanzu haka yankin saharar Afrikan na da masana ko kuma kwararru a fannin samar da lantarkin ta hanyar hasken rana kasa da sufuri da adadin mutane dubu 16 kacal da ke aiki a sashen AFP
Talla

Rahoton da gidauniyar Thomson Reuters ta fitar a yau ta ce yanzu haka kasashen yamma da saharar Afrikan na fuskantar karancin kwararru a fannin samar da lantarkin ta hasken rana da ma karancin masu kula da shi duk da cewa kuwa yanzu ita ce hanya mafi sauki da kasashen kan yi amfani da ita don samun lantarki.

Rahoton ya bayyana cewa yanzu haka yankin saharar Afrikan na da masana ko kuma kwararru a fannin samar da lantarkin ta hanyar hasken rana kasa da sufuri da adadin mutane dubu 16 kacal da ke aiki a sashen.

Ko da dai fasahar samar da lantarkin ta hanyar hasken rana na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi a nahiyar ta Afrika rahoton ya ce har yanzu akwai karancin matasa da ke da sha’awar samun horo akansa duk kuwa da samar da manyan kamfanoni a kasashe 12 ciki har da Rwanda da Pakistan.

A tashar samar da lantarkin da hasken rana da ke Goma a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo mafi girma a kasar, akwai gagarumin kalubale a cewar shugaban sashen Kweku Yankson, haka zalika wadda ke Rwanda inda ake da karancin ma’aikata.

Matakin gaza inganta sashen a cewar gidauniyar babban koma baya ne ga nahiyar idan aka kwatanta da India wadda ke shirin horar da mutane dubu 50 nan da shekarar 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.