Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

An tantance sunayen 'yan takara a zaben Congo

Hukumar zaben Janhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta bayyana sunayen wadanda suka cancanci tsayawa takarar zaben shugaban kasar da za’a yi cikin watan Disamba mai zuwa.

Shugaban hukumar zaben Congo, Corneille Nangaa, ranar 5 ga watan nuwamba 2017 a Kinshasa
Shugaban hukumar zaben Congo, Corneille Nangaa, ranar 5 ga watan nuwamba 2017 a Kinshasa © JOHN WESSELS / AFP
Talla

Shugaban hukumar zaben kasar Corneille Nangaa yace bayan tantance sunayen yan takarar zaben yanzu zasu mayar da hankali ne kan shirin zaben gadan gadan.

 

Cikin yan takarar da suka tsallake siradin hukumar sun hada da Felix Tsekeshedi, da Vital Kamerhe da kuma tsohon ministan cikin gida Emmanuel Ramazani Shadary da ke samun goyan bayan shugaba Joseph Kabila.

 

Sunayen sun kuma tabbatar da haramcin da aka yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa Jean-Piere Bemba da kuma Moise Katumbi, wadanda kotun koli ta soke halascinsu.

Tarihi ya nuna cewa, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ba ta taba gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali ba tun bayan samun ‘yancin kan kasar daga Belguim a shekarar 1960.

Za a yi zaben ne a ranar 23 ga watan disamba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.