Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Jam'iyyar ANC za ta zabi sabon shugaba

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya ce al’ummar kasar ba su ji dadin mulkin Jam’iyyar ANC ba, Kalaman da ke zuwa a dai-dai lokacin da aka bude babban taronta na kasa da za a share tsawon kwananki 5 ana yi domin zaben sabon jagora.

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma
Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Manyan ‘yan takarar shugabanci jam’iyyar sun hada da tsohuwar shugabar kungiyar kasashen Afrika, AU, Dlamini-Zuma da mataimakin shugaban kasa Cyril Ramaphosa wanda attajirin dan kasuwa ne.

Taron mai tattare da kalubali duk wanda ya yi nasaran lashe kujerar shugabanci jami’iyyar shi zai kasance dan takarar shugaban kasar da za a gudanar a shekara ta 2019.

Shugaba Jacob Zuma da badakalar rashawa ta dabai-baiye gwamnatinsa, zai sauka daga shugabanci Jam’iyyar bayan zaben sabon shugaba, sai dai zai ci-gaba da mulkinsa har zuwa lokacin baban zaben kasar.

Karuwar Rashin aikinyi da Rashawa su ne muhimman batutuwan da suka haifar da koma baya ga gwamnatin Zuma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.