Isa ga babban shafi
Liberia

Kotun kolin Liberia ta bayyana cewa za 'a gudanar da zagaye na biyu na zaben kasar

Kotun koli Liberia ta yi watsi da zargin da ake yi ne cewa hukumar zaben kasar ta tafka magudi a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Alkalan kotun kolin Liberia tareda Shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf
Alkalan kotun kolin Liberia tareda Shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf Supreme Court of Liberia
Talla

Bayan jinkarta zagaye na biyu na zaben da ya kamata a fafata tsakanin Joseph Boakai na jam’iyyar mai mulki da George Weah a ranar 7 ga watan Nuwamba,a jiya alhamis kotun kolin Liberia ta bayyana cewa za a gudanar da zagaye na biyu na zaben Shugaban kasar.

Charles Brumskine na Jam’iyyar Liberty da ya zo na Uku a zaben ne ya shigar da korafin da ya yi sanadi jinkirta zaben.

Sai dai hukumar zaben kasar ta ce jam’iyyu da ke zargin an aikata magudi sun gaza gabatar da hujojjin da ke tabbatar da hakan.

Kafin wannan sanarwa, Jam’iyyun da suka shigar da kara sun bukaci jami’an hukumar zaben kasar suyi murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.