Isa ga babban shafi
Tarayyar Afrika

Afrika: Mutane miliyan 380 zasu nemi aikin yi nan da shekarar 2030

Hukumar bunkasa ayyukan noma ta majalisar dinkin duniya ta ce kimanin mutane miliyan 380 ne za su shiga cikin jerin masu neman aiki a yammacin nahiyar Afirka nan da shekara ta 2030.

Wasu matasa 'yan Afrika da ke kokarin tsallakawa zuwa kasashen ketare domin samun ayyukan yi, ta hanyar bi ta kasar Libya.
Wasu matasa 'yan Afrika da ke kokarin tsallakawa zuwa kasashen ketare domin samun ayyukan yi, ta hanyar bi ta kasar Libya. REUTERS/Hani Amara
Talla

A cewar hukumar, akwai babban kalubale dangane da yadda za a samar da guraben ayyuka ga wadannan mutane.

Cikin sanarwar da hukumar ta bayar ya nuna cewa ya kamata a rika sanya aikin noma a cikin matakan da za a dauka domin magance kalubalen da hijirar mutane ke haifarwa.

Hukumar wacce ta fitar da bayanin ta hanyar yin nazari daga mawallafa daban daban na hukumomin bincike da hukumomi na kasashen duniya, ta ce kimanin miliyan 220 daga cikin mutanen da za su fantsama cikin neman aiki nan da shekara ta 2030 zasu fito ne daga yankunan karkara.

Mataimakin darakta janar na kukumar ta FOA Kostas Stamoulis, ya ce yawan al’umma a yankin yammacin nahiyar Afirka ya karu da miliyan 645 a tsakanin shekarun 1975 da 2015.

Ya kara da cewa a yankin ne kawai yawan al’umma na yankunan karkara zai cigaba da habbaka bayan shekara ta 2050, a cikin fadin duniya, wanda ya ce hakan zai kara kawo matsi a bangaren noma, dan haka dole a fadada hanyoyin samun kudaden shiga.

A cewar rahoton yawancin wadanda za su yi hijira a cikin shekarun da aka ayyana, matasa ne wadanda suka fito daga yankunan da aka fi yin riko da sana’ar noma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.