‘Yan adawa sun bukace a dage zaben Guinea
‘Yan adawa a kasar Guinea Conkry sun bukaci a dage gudanar da zaben shugabancin kasar da ya kamata a yi a ranar 11 ga wannan wata wannan oktoba da akalla mako daya, domin bai wa hukumar zabe damar kara kintsawa.
Wallafawa ranar:
A cewar Faya Francois Bruno, mai magana da yawun ‘yan adawar manyan dalilan su na dage zaben, sun hada da rashin kintsawa wannan zabe, raba katunan zabe bisa rashin tsari a kasar, kuma akwai dimbin jama’ar da suka yi rejista amma har zuwa wannan lokaci ba su samu katunansu.
Faya ya kuma kara da cewa Har ila yau suna da shakka a game da wasu kamfanonin daba’i da aka bai wa kwangilar buga katunan zabe.
Sannan akwai matsala dangane da yawan wadanda suka cancanci jefa kuri’a, a wasu rumfana za a tarar cewa akwai dimbin jama’a yayin da a wasu yankunan yawan masu kada kuri’a bai taka kara ya karya ba.
Abin da suka bayyana cewa ba su yarda da shi ba,Saboda haka suka bukaci a dage wannan zabe da akalla mako daya, domin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu