Isa ga babban shafi
Duniya

Kusan mutane dubu 1 da 300 ne suka kamu da cutar coronavirus

Wasu alkaluma daga hukumar lafiya  na nuni cewa akalla mutane kusan 1.300 ne suka kamu da cutar coronavirus ko Mashako a kasar China ,yayinda aka bayyana mutuwar wasu mutanen 41 tun bayan bulluwar wannan cuta.

Daya daga cikin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a China
Daya daga cikin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a China reuter
Talla

Hukumar lafiya ta Duniya WHO na ci gaba da yin kira ga hukumomin kasashen Duniya don ganin sun dau matakan da suka dace na kariya  da kamuwa da kwayar cutar coronavirus ko Mashako kamar dai yada bincike ya tabbatar.

Baya ga kasar ta China kwayar cutar coronavirus ta  bullu a wasu kasashen Turai da suka hada da Faransa,da Austria.

A Faransa mutane uku ne Ministar kiwon lafiya ta bayyana sun kamu da cutar coronavirus,yayinda a Austri mutum daya aka  gano cewa ya na dauke da kwayar cutar.

Japan,Amurka,Nepal,Singapor,Taiwan,Thailand, Hong Kong, Macao da Vietnam na daga cikin kasashen da aka gano cewa mutane na daukje da kawayar cutar ta coronavirus ko Mashako.

Akasar ta China hukumomin sun aike da sojoji zuwa yankunan da cutar coronavirus ta fi muni musaman yankin Wuhan,inda aka bayyana sake gina wani sabin asibiti da zai daukar nauyin mutanen da suka kamu da cutar ta coronavirus a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.