Isa ga babban shafi
Faransa

An lalata kaburburan Yahudawa a Faransa

Rahotanni daga Faransa sun ce akalla kaburbura sama da 100 na Yahudawa ne aka lalata a kusa da Strasbourg dake gabashin kasar, a wani yunkuri na nuna wariya a gare su.

Kaburburan Yahudawa da aka lalata a Faransa
Kaburburan Yahudawa da aka lalata a Faransa Frederick FLORIN / AFP
Talla

Shugaban kungiyar Yahudawa dake Faransa, Maurice Dahan ya bayyana kaduwa da matakin, inda ya bukaci hukumomi su dauki mataki akai.

Shugaba Emmanuel Macron da ya ziyarci wurin domin gani da idon sa, ya sha alwashin magance matsalar kalaman batunci da kuma fadakar da daliban makarantu muhimmancin watsi da shi.

Gwamnatin Faransa ta sanar da daukar matakan hukunta masu aikata irin wadanan ayuka dake tayar da hankulan jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.