Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/02 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 20/02 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/02 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 20/02 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/02 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 20/02 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/02 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 20/02 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/02 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/02 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/02 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/02 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/02 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/02 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 20/02 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/02 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 19/02 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/02 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 19/02 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Yankin Hausawa

Mourinho ya maye gurbin Pochentino

media José Mourinho sabon mai horar da kungiyar Tottenham Reuters/Carl Recine/File Photo

Dan kasar Fotugal Jose Mourinho ya maye gurbin dan kasar Argentina Maurico Pochentino da kungiyar kwallon kafar Tottenham ta yi waje da shi.

A sanarwar da kulob din na Tottenham ya fitar,cimma wannan yarjejeniya da Mourinho na da nasaba da irin rawar da ya taka a baya kasancewa ya taba horar da kungiyoyi da suka hada da Chelsea da Manchesterd United a gasar Premier ta Ingila kamar dai yada kamfanin dilanci labaren Faransa na AFP ya ruwaito.

Sanarwar da kungiyar ta gabatar yace Mourinho wanda tsohon mai horar da kungiyoyin Chelsea da Manchester United ne, ya sanya hannu kan kwangilar da zata kais hi zuwa karshen kakar shekarar 2022 zuwa 2023.

Shi dai Pochettino mai shekaru 47 ya fara aiki ne da Tottenham Hotspur a shekarar 2014 bayan ya bar kungiyar Southampton, inda ya sauya alkiblar kungiyar ta zama daya daga cikin wadanda ake tinkaho da su a Ingila da kuma gasar cin kofin zakarun Turai, inda suka kai matakin karshe a karon farko.

Matsalolin da kungiyar ta samu a kakar bana wanda ya bar ta a matsayi na 14 a teburin Premier da kuma samun maki 3 kacal daga wasanni 12 da ta buga, ya harzuka shugabannin kungiyar da magoya bayan ta.

Tuni dai aka fitar da kungiyar Tottenham daga League Cup yayin da Bayern Munnich ta yiwa kungiyar cin kaca 7-2 a gasar cin kofin Turai.

Tuni Mourinho ya bayyana farin cikin sa da nadin da aka masa, inda ya bayyana gamsuwa da zaratan Yan was an dake kungiyar da kuma bangaren yaran da ake horar wa.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure