Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya sake fadawa wani sabon rikici

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy dake fuskantar tuhumar karban kudaden yakin zabe ta hanyar da bata kamata ba, yanzu haka ya fada cikin wani sabon rikicin karbar wasu kudade da aka kaddamar da bincike a kai.

Hoton zane mai motsi na Sarkozy da marigay Kadhafi
Hoton zane mai motsi na Sarkozy da marigay Kadhafi Crédits: Editions Delcourt/La revue dessinée
Talla

Ma’aikatar shari’ar Faransa ta tabbatar da binciken wata kafar yada labaran intanet, wato Mediapart dake nuna cewar, ofishin yaki da cin hanci da rashawa na gudanar da bincike kan tsohon shugaban kasar da yayi mulki tsakanin shekarar 2007 zuwa 2012.

Mediapart tace wani bincike da jami’an tsaro suka gudanar gidan wani dillalin kayan tarihi, Christian Deydier, an gano wata takardar ajiyar banki dauke da sunan tsohon shugaban Nicolas Sarkozy.

Takardar da aka gano na daga cikin binciken da ake cewar tsohon shugaban Libya Muammar Ghadafi ya bada kudi euro 2,000 domin sayen kayan tarihi da sunan Sarkozy.

Tambayoyi sun nuna cewar, wani na hannun Sarkozy na zuwa banki kowane wata inda yake karbar euro 2,000 da ake dangantawa da tsohon shugaban, abinda ya saba kai’da.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.