Isa ga babban shafi
Turai

Kungiyar da zata lashe kofin zakarun Turai a yau?

Kungiyoyin kwallon kafa na Liverpool da Tottenham za su kara da juna a yau asabar a kofin zakarun Turai da zai gudana a Madrid na kasar Spain.

Gasar cin kofin zakarun Turai
Gasar cin kofin zakarun Turai Reuters
Talla

Tottenham dai wannan ne zai zamo mata karon farko da za ta taba buga wasan karshe na cin kofin zakarun turai, yayinda ita kuma Liverpool ko a bara ta kai matakin amma Real Madrid ta yi nasara da kwallaye 3 da 1.

Tuni dai masana wasanni suka fara sharhi kan wasan na yau, wanda ake ganin ba mai sauki ba ne la'akari da yadda kungiyoyin biyu ke kusan matsayin karfi guda, inda ko a wasannin su na Firimiya su kan yi canjaras a lokuta da dama.

Wasan dai tsakanin Liverpool da Tottenham zai zamo irinsa na uku da kungiyoyin Ingila biyu za su kara da juna a wasan na yau babbar gasa a nahiyar Turai, wato tun bayan wasan karshe na cin kofin UEFA tsakanin Tottenham da Wolves a shekarar 1972 da kuma wasan karshe na cin kofin zakarun turai a shekarar 2008 tsakanin Man United da Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.