Isa ga babban shafi
Amurka

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis ya yi marabus

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis ya yi marabus daga mukaminsa don nuna rashin amincewa da matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na janye dakarun kasar baki daya daga Syria da kuma rage wani adadi na sojojin daga Afghanistan.

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis
Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Mattis ya bayyana hakan ne a cikin wasikar da ya rubutu wa shugaba Trump, a daidai lokacin da kasashen yammacin duniya kawayen Amurka ke nuna rashin amincewarsu da janyewar wadannan dakaru lura da cewa har yanzu ba a murkushe kungiyar IS ba.

Faransa da Birtaniya sun lashi takobin ci gaba da wanzar da dakarunsu a Syria, sun ce, har yanzu akwai-sauran -rina-a-kaba a yaki da Kungiyar ISIS, sabanin ikirarin Trump da ke cewa, an ci karfin ta.

Kimanin dakarun Amurka dubu 2 ke jibge a Syria, in da akasarinsu ke aikin bada horo da shawarwarin da ke taimaka wa dakarun kasar wajen yaki da Kungiyar ISIS, yayin da Birtaniya da Faransa ba su bayar da alkaluman nasu dakarun da ke cikin kasar ba.

Mai magana da yawun Firaministar Birtaniya ya ce, za su ci gaba da nuna goyon baya ga rundunar hadaka ta kasashen duniya da zummar murkushe yunkurin ISIS na kafa daula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.