A shirin namu na yau zai karkata ne zuwa kasar Kamaru, inda zai duba tarihin kabilar hausawa daya daga cikin kabilu Kamaru sama da 200 da Allah ya zuba a kasar, kabilar da ake samu a kasashe da dama na Afrika da suka hada da Najeriya,Nijar, Ghana, Tchad, Sudan, Jamhuriya Afrika ta tsakiya .Shirin al’adun mu na gado shirin da kan tattauna lamarun da suka shafi al’adu a Duniya tare da Mahaman Salisu Hamisu.
Sauran kashi-kashi
-
Tasirin masu sarautar gargajiya wajen inganta tsaro a yankunansu
A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976, aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha’anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari’ah da kuma batun tara haraji a cikin al’ummarsu.Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al’amura.05/03/202410:02 -
Yadda sana'ar rini ke bacewa sannu a hankali a arewacin Najeriya
Shirin 'Al'adun Gargajiya' na wannan makon tare da Abdullahi Issa ya maida hankali ne kan bacewar sanar gargajiya ta rini a jihar Kano dake arewacin Najeriya, kafin daga bisa shirin ya leka Maradi dake jamhuriyar Nijar.14/11/202310:19 -
Bafaranshiya ta lashe kyautar iya gasa biredi ta duniya
Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya tabo batun kyautar da matashiya 'yan Farsans ta lashe, inda ta zamo ta daya a duniya a wannan shekarar wajen iya gasa biridi. Tarihi dai ya nuna wannan ne karo na faro da mace ta taba lashe wannan kyauta.31/10/202310:31 -
Shekaru 30 na Sarkin Masarautar Zazzau Suleja
Shirin Al'adunmu na wannan mako ya yada zango ne Masarautar Zazzau Suleja ta jihar Neja dake Najeriya domin shaida bikin murnar cika shekaru 30 na Sarkin Masarautar mai dimbin tarihi, Mallam Muhammadu Auwal Ibrahim, wanda ya kasance gwamnan jihar na farko na farar hula a jamhuriya ta biyu daga shekarar alif 979 zuwa alif 983.17/10/202310:00 -
Yadda harshen Hausa ke samun karbuwa a jami'o'in Burkina Faso
Shirin ala'dun mu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan taron inganta harshen Hausa da aka shirya a jami'ar Ouagadougou da ke Burkian Faso26/09/202310:02