Isa ga babban shafi
Faransa

An tura karin masu aikin ceto zuwa Aude na Faransa

Akalla mutane 13 sun rasa rayukansu sakamakon amabaliyar ruwa da ta afkawa yankin kudu maso yammacin Faransa.Hukumomin Kasar sun ce a shekaru da dama da suka gabata ambaliyar ce mafi muni da ta taba faruwa a kasar.

Yankin Aude na kasar Faransa da aka samu ambaliya
Yankin Aude na kasar Faransa da aka samu ambaliya Pascal PAVANI / AFP
Talla

Ruwan sama da aka tafka a yankin Aude na kasar Faransa a cewar hukumomin za a iya kwantata su da ruwa na watanni uku cikin dare daya.

Ambaliyar ta shafe yankuna da dama tareda tilastawa da dama daga cikin mazauna wadanan yankuna ficewa daga gidajen su, bayan da aka kiyasta asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.

Fadar Shugaban kasar faransa ta sanar da cewa shugaba Emmanuel Macron zai ziyarci yankin Aude yayinda Firaministan Kasar, Edouard Philippe ya isa yankin domin jajintawa mutane da lamarin ya rutsa da su.

A kokarin ta na kai dauki gwamnatin Faransa tareda \hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kan su ta aike da karin jami’an kwana kwana 300, da wasu jami’an tsaro 400 da za su dafawa masu aikin ceto a Aude.

A mataki na kwantar da hankulan jama’a mahukuntan kasar sun bukaci jama’a da su kasance a gidajen su yayin da aka sanar da rufe makarantu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.