Isa ga babban shafi
Sudan

Karin dakaru 150 zuwa jihar Unity da ke Sudan ta Kudu daga MDD

Majalisar dinkin duniya ta aike da dakarunta 150 zuwa jihar Unity da ke Sudan ta Kudu, domin kare fararen hula, wadanda yakin da ake gwabzawa tsakanin sojin gwamnati da ‘yan tawaye ke shafa.Majalisar ta ce matakin zai bada damar kawo karshen laifukan yakin da ake aikatawa a kauyuka da dama na jihar.

Wasu daga cikin mayakan dake dafawa bangaren adawa na Sudan
Wasu daga cikin mayakan dake dafawa bangaren adawa na Sudan REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Daga shekarar 2013 zuwa yanzu akalla mutane miliyan 1 da dubu 700 ne suka rasa muhallansu, a dalilin gwabza kazamin yaki tsakanin sojin gwamnati da mayakan madugun ‘yan tawaye kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar.

Kasashen Duniya na cigaba dakira zuwa masu ruwa da tsaki a rikicin kasar , sai dai hakar su ba ta cimma ruwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.