Isa ga babban shafi
Chadi-Najeriya-Nijar

Dakarun Chadi sun fatataki yan Kungiyar Boko Haram

Sojojin Chadi sun kaddamar da wani gagarumin farmaki akan mayakan Boko Haram a wasu kauyuka da ke kusa da tafkin Chadi kamar dai yadda shaidu suka sanar.Wannan nasara na zuwa ne yan kwanuki bayan da Rundunar sojan Nigeria ta 7 da ke Maiduguri ta ce dakarun kasar sun kwato garin Dikwa da ke jihar Borno, bayan da garin ya share watanni da dama a hannun ‘yan kungiyar boko haram.

Kakakin rundunar Sojin Chadi Toma Hounou da ke fada da Mayakan Boko Haram na Najeriya
Kakakin rundunar Sojin Chadi Toma Hounou da ke fada da Mayakan Boko Haram na Najeriya
Talla

Rahotanni sun ce tun a jiya litinin ne dakarun na Chadi suka fara kai hare-haren a yankin da ke cikin kusurwar da ta hada iyakokin kasashen Nigeria, Niger, Kamaru da kuma Chadi, yankin da ake kallo a matsayin babbar maboyar magoya bayan Boko haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.