Isa ga babban shafi
Birtaniya

Kamfanin Google ya bayyana a gaban Majalisar Birtaniya kan batun kaucewa biyan haraji

Wata babbar ‘yar Majalisa a kasar Birtaniya ta bayyana Kamfanin Google a matsayin Shaida,. inda ta kuma bayyana jami’an leken Asiri na Amurka a bangaren Yanar Gizo da cewar sun karya ka’idar aikin su ta hanyar kaucewa biyan Haraji a kasar Birtaniya.

Tambarin Kamfanin Google
Tambarin Kamfanin Google AFP/Nicholas Kamm
Talla

Wannan ‘yar Majalisar mai suna, Margaret Hodge shugabar wani Kwamiti ce mai kula da harkokin yada Labarai ta Majalisar kasar ta Birtaniya ta kalubalanci mataimakin shugaban kamfanin na Google, Matt Brittin da cewar basa aiki kamar yadda ya kamata.

Sai dai a lokacin da shugaban Kamfanin na Google ke gabatar da jawabbansa, ya musanta batun yin wata dabarar kaucewa biyan harajin ga kasar ta Birtaniya.

Hodge ta cewa Kamafanin Google ya yi ikrarin cewar baya aikata Assha, amma kuma ya labe ga wata kisisiniya yana aikata ta’asa.

Amma kuma a cewar ta sun ga hujjoji a fili da suka nuna cewar Google baya da kirki wajen biyan haraji.

Shi kuma mataimakin shugaban Kamfanin ya tsaya Kai da Fata cewar sun bi duk tanadin Doka da ‘yan Siyasa suka gindaya masu, kuma ai biyan Haraji ba zabi ba ne, abu ne daya shafi Dokar Kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.