Isa ga babban shafi
Wasan Tennis

Zai yi wuya na halarci gasar French Open- Murray

Dan wasan Tennis na biyu a duniya, Andy Murray ya ce akwai yiwuwar ba zai halarci gasar French Open ba bayan wani ciwo a bayansa da ya tilasta mai ya fice daga gasar Rome Masters da ake bugawa a kasar Italiya.“Zan yi mamaki kwarai idan har na samu damar halartar gasar French Open na bana.” Inji Murray.  

Dan wasan Tennis Andy Murray na Birtaniya
Dan wasan Tennis Andy Murray na Birtaniya REUTERS/Daniel Munoz
Talla

A cewar Murray ciwon bayan ya jima yana addabarsa tun a shekarar 2011, wanda yake kara tsananta a ‘yan kawanakin nan.

Sai dai a daya bangaren, Rafeal Nadal wanda ya lashe Madrid Masters na cigaba da samun nasara a gasar ta Rome Masters bayan ya doke Fabio Fognini dan kasar Italiya da ci 6-1,6-3.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.