Isa ga babban shafi
China/Sin

Adadin wadanda suka mutu a girgizan kasar China ya haura 200

A yayin da ake cigaba da gudanar da ayyukan ceto domin kubuto wadanda girgizan kasa a China ta rutsa da su, rahotanni na nuna cewa adadin wadanda suka mutu ya haura mutane 200. Hadarin ya auku ne a Kudu maso Yammacin yankin kasar ta China, a yayin da sama da mutane 1,000 suka jikkata sannan wasu sama da miliyan daya suka rasa matsugunansu.  

Masu ba da agajin gaggawa suna taimakon wadanda girgizan kasar ta afka da su
Masu ba da agajin gaggawa suna taimakon wadanda girgizan kasar ta afka da su pbs.twimg.com
Talla

An dai kiyasta karfin girgizan kasar ya kai karfin maki 6.6, wannan itace kuma girgizar kasa mafi muni da kasar ta fuskanta cikin shekaru uku da suka shude, wacce ta auku a yankin Lushan inda nan ne aka fi samun mace mace da dama.

Rahotanni na nuna cewa masu ayyukan ceto na fuskantar matsaloli wajen gudanar da ayyukansu saboda tsukukun hanyoyi da yankin na Lushan ke da shi, hakan kuma kawo tsaiko wajen raba kayyayakin agaji ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

“Kayayyakin agaji bas u samu isa ga yankin ba saboda yawan cunkoso, mafi aksarin kayyayakinmu suna kan hanya a tsaye.” Inji Kevin Xia, wani Jami’in bad a agajin gaggawa na Red Cross.

Ma’aikat ayyukan cikin gida ta kasar ta China ta bayyana cewa mutane 184 suka rasa rayukansu a yayin da wasu 24 ba a san inda suke ba, sannan 18,000 sun jikkata.

Sai dai rahotannin baya bayan nan na nuna cewa adadin mutanen da suka rasu ya kai 208.

A shekarar 2008, girgizan kasa mai karfin maki 7.9 ta abkawa kasar ta China inda aka yi kiyasin mutane sama da 70,000 ne suka mutu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.