Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Fafaroma Francis na Daya ya karbi karfin ikon gudanar da jagoranci

Fafaroma Francis na Daya, ya karbi karfin ikon gudanar da jagorancinsa a matsayin shugaban mabiya darikar Katolika na duniya. Daga cikin ire-ire abubuwan da ya karba a mazaunin madafar iko, har da zobe da kuma wani nau’in yadi dake nuna Fafaroman a matsayin mai jagoranci jama'a, sannan zoben alama ce da ke nuna taka rawar da Fafaroman farko a duniya, St Peter ya yi, wanda asalin sana’arsa kamun kifi ne. 

Fafaroma Francis na Daya
Fafaroma Francis na Daya REUTERS/Vatican CTV via Reuters
Talla

An kaddamar da Fafaroman ne a gaban dubban mutane a taron wanda aka gudanar da shi a dandalin St. Peter’s dake Fadar ta Vatican, wanda har ila yau ya samu halartar shugabannin kasashen duniya da dama.

Rahotanni na nuna cewa, anga Fafaroma Francis ya tsuguna a bakin kabarin St. Peter, inda ya addu'a, bayan ya wuce cikin wata tawaga kamin ya karasa bakin kabarin na St. Peter.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.