Isa ga babban shafi
Wasanni

La Liga ta cuce mu- Leganes

Leganes ta ce, Hukumar Kwallon Kafar Spain ta haddasa mata 'mummunar barna' bayan hukumar ta yi watsi da bukatar kungiyar ta maye gurbin Martin Braithwaite.

Martin Braithwaite da ya koma Barcelona daga Leganes a ranar 20 ga watan Fabairu
Martin Braithwaite da ya koma Barcelona daga Leganes a ranar 20 ga watan Fabairu Skysport.com
Talla

Braithwaite mai shekaru 28 ya koma Barcelona daga Leganes a ranar 20 ga watan Fabairu domin cike gurbin da Osumane Dembele ya bari saboda rauni, inda zai yi zaman jinyar makwanni shida.

Dokokin La Liga sun bai wa duk wata kungiya damar maye gurbin dan wasan da zai yi jinyar fiye da watanni biyar, amma a yanzu ita Leganes ba ta damar maye gurbin Braithwaite saboda haramun ne ta yi cefenen dan wasan bayan rufe kasuwar musayar ‘yan wasan.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Leganes ta bayyana matakin a matsayin rashin adalci a gare ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.