Isa ga babban shafi
Wasanni

City ta kafa tarihin samun nasarar farko kan Real Madrid

Manchester City ta kafa tarihin doke Real Madrid karo na farko a gasar Zakarun Turai, bayanda a ranar laraba ta yi tattaki har filin wasa na Santiago Bernabeu a Spain, ta doke Madrid da kwallaye 2-1.

Yan wasan Manchester City yayin murnar samun nasara kan Real Madrid a Spain.
Yan wasan Manchester City yayin murnar samun nasara kan Real Madrid a Spain. REUTERS/Sergio Perez
Talla

Real Madrid ce ta soma jefawa Manchester City kwallo ta hannun dan wasanta Isco, daga bisani ne kuma ‘yan wasan City Gebriel Jesus da Kevin de Bruyne suka jefa kwallayen biyun da suka basu nasarar farko kan Real Madrid a gasar ta Zakarun Turai.

Kafin fafatawar ta baya bayan nan sau 4 kungiyoyin suka hadu a gasar Zakarun Turai cikin shekarun 2012 da kuma 2016, inda Real Madrid ta yi nasara sau 2, suka kuma yi canjaras a sauran wasannin 2.

Wani batu da ya dauki hankali a wasan shi ne yadda fitaccen mai tsaron bayan masu masaukin bakin wato Sergio Ramos ya samu jan kati, abinda wasu masharhanta ke ganin zai haifar wa da kungiyar ta Real Madrid nakasu yayin fafatawa zagaye na biyu da za su yi tattaki zuwa Ingila don maidawa City biki a filin wasanta na Etihad, ranar 17 ga watan Maris mai kamawa.

A halin yanzu Sergio Ramos ya shiga sahun ‘yan wasan da suka fi karbar jan kati a gasar Zakarun Turai bayan na ranar larabar da ya karba dake a matsayin na 4, adadi guda da wadanda Edgar David da Zlatan Ibrahimovic ke da su a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.