Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Sharapova ta yi bankwana da fagen Tennis

An haife  Sharapova Maria  ranar 19 ga watan Afrilun shekarar 1987, a yau ta na mai shekaru 32 da haifuwa.An kuma haife ta a garin Nyagan dake kasar Rasha ta na kuma zaune a kasar Amurka musaman yankin Bradenton dake Florida. Sharapova ta samu nasarori 645, yayinda aka kuma bayyana rashin nasarori ko kalubale da ta fuskanta iya rayyuwar ta na yar wasa 171.

Maria Sharapova yar wasar Tennis da ta sanar da ritaya daga fagen Tennis
Maria Sharapova yar wasar Tennis da ta sanar da ritaya daga fagen Tennis REUTERS/Aly Song
Talla

Ta lashe kofuna sau 36, a gasar Olympics na shekara ta 2012 ta lashe azurfa.

Yar wasar Tennis Maria Sharapova a yau ta sanar da yin ritaya daga fagen Tennis da ta shiga tun a shekara ta 2001.

Ta na daga cikin ziratan yan wasan Tennis bangaren mata da aka sani a Duniya,baya ga yan wasa irin Su Serena Williams, Ashleigh Barty yar kasar Austria,Elena Rybakina da su Aryna Sabalenka yar kasar Belarusse.

Yanzu haka ana bayyana cewa ta samu kusan milyan 38 da dubu 777 da kuma yan canji na dalla tsawon lokaci da ta share ta fagen Tennis.

Yayinda Maria Sharapova ke bankwana da fagen Tennis,ana fafatawa yanzu haka a gasar cin kofin Tennis na Doha .

Mu soma da bangaren mata

Ashleigh Barty yar Austria ta doke Elena Rybakina daga Kazhakstan.

Petra Kvitová yar Czeck ta doke Jelena Ostapenko 6-2, 5-7, 6-1

Svetlana Kuznetsova daga Rasha ta doke Amanda Anisimova daga Amurka.

Aryna Sabalenka yar yankin Belarusse ta dioke Maria Sakkari daga Girka 6-3, 6-0

Bangaren maza

Karen Khachanov daga Rasha ya doke Dennis Novak daga Austria 6-3, 6-4

Andrey Rublev daga Rash aya lallasa Filip Krajinovic daga Sabiya) 7-6 (7/3), 6-0

Daniel Evans daga Birtaniya ya doke Pierre-Hugues Herbert daga Faransa 7-5, 3-6, 7-6 (9/7)

Jan-Lennard Struff daga Jamus ya doke Nikoloz Basilashvili daga Geogia 6-1, 6-0

Stefanos Tsitsipas daga Girka ya doke Alexander Bublik Kazhakstan 7-6 (7/1), 6-4

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.