Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Chelsea za ta kara da Bayern ba N'Golo Kante

Yau kungiyar Chelsea zata kari bakuncin Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, a matakin zagaye na biyu.

N'Golo Kanté,dan wasan Chelsea
N'Golo Kanté,dan wasan Chelsea Benjamin CREMEL / AFP
Talla

A karawar da za’ayi yau, Chelsea ba zata iya sanya dan wasan ta na tsakiya, N’Golo Kante ba, saboda raunin da ya samu wanda zai hana shi wasanni na makwanni uku.

Ana kuma shakkun cewar ‘yan wasa irin su Christian Pulisic da Pedro da Cullum Hudson-Odoi ba zasu damar shiga karawar da za’ayi yau ba, sai dai Ruben Loftus-Cheek wanda ya dawo daga raunin da ya samu.

Ita ma kungiyar Bayern ba zata sanya Niklas Sule da Ivan Perisic ba saboda raunin da suke fama da shi.

Wannan wasa na da matukar muhimmanci ga kungiyoyin biyu.

A karawar da kungiyoyin biyu suka yi a irin wannan gasa a shekarar 2012, Chelsea ta doke Bayern da ci 4-3.

Tauraron Bayern Robert Lewandoski ya zirara kwallaye 10 a gasar bana shi kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.