Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Ban san ran da Hazard zai dawo ba - Zidane

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya ce ba shi da tabbacin ko dan wasan gabansa, Eden Hazard zai sake murza leda har zuwa karewar wannan kaka, kuma ya kare irin yadda kungiyar ke bullo wa al’amarin raunin da ya samu a idon sawunsa.

Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane.
Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane. REUTERS/Juan Medina
Talla

Dan kasar Belgium din ya fita daga filin wasa da dingishi bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a wasan da Madrid ta yi rashin nasar 1-0 a gidan Levente ranar Asabar, washegari ne kuma gwajin da aka wa dan wasan ya tabbatar da cewa ya samu karaya a idon sawu.

Madrid dai ba ta sanya wata rana da take ji Hazard zai dawo filin tamaula ba, kuma rashinsa babban nakasu ne ga wasan da za ta fafata da Manchester City a tsakiyar mako a wasan gasar zakarun nahiyar Turai, da kuma wasan hamayya ta El Clasico da Barcelona a ranar Lahadi.

Kwanan nan ne dai dan wasan mai shekaru 29 ya dawo daga jinyar tsawon watanni 3 sakamakon wani rauni makamancin wannan, saboda haka ne ma a wani taron manema labarai mai horar da kungiyar Zidane ya ce bai san ran da dan wasan zai dawo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.