Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

'Yan wasana ba su taka rawar gani ba - Solskjaer

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce ‘yan wasan sa ba su taka rawar gani ba a wasan da suka gwabza da Club Brugge ta kasar Belgium a daren Alhamis, wasan da aka tashi kunnen doki 1-1.

Kocin Manchester United manager Ole Gunnar Solskjaer.
Kocin Manchester United manager Ole Gunnar Solskjaer. REUTERS/Andrew Yates
Talla

Manchester United ba ta fara wasan da armashi ba, saboda kafin ta Ankara a farkon wasan, Emmanuel Dennis ya antaya mata kwallo a raga.

Anthony Martial ya cire wa United kitse a wuta, inda ya farke mata wannan kwallo, bayan wani fito na fito da ya yi da tsohon mai tsaron ragar Liverpool, Simon Mignolet, mai tsaron ragar Brugge na yanzu.

Solskjaer ya ce bai ji dadin wasan ba, sai dai duk da haka ya nuna alamun farin ciki da kwallo daya da kungiyar ta samu a waje.

Kocin ya bayyana kwarin gwiwar make kungiyar idan ta mayar da biki a mako mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.