Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool na shirin raba gari da Adam Lallana

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool na shirin raba gari da Adam Lallana a karshen wannan kaka dai dai lokacin da kwantiraginsa dan wasan tsakiyar mai shekaru 31 ke shirin karewa a karshen kakar.

Adam Lallana yayin karawar Liverpool da Everton karkashin wasannin gasar Firimiya.
Adam Lallana yayin karawar Liverpool da Everton karkashin wasannin gasar Firimiya. REUTERS/Phil Noble
Talla

Lallana wanda ya kulla kwantiragin shekaru 6 da Liverpool a shekarar 2014, kawo yanzu babu maganar sabunta kwantiragi tsakaninsa da Reds matakin da ke nuna cewa yana da ‘yancin kulla kwantiragi da wani club din cikin sauki a karshen kaka.

Adam Lallana dan ingila wanda Liverpool ta sayo daga Southampton kan yuro miliyan 25 akwai rade-radin yana shirin kulla kwantiragi ne da Leicester City a sabuwar kakar wasa.

Cikin wannan kaka dai, Lallana ya dokawa Liverpool mai rike da kambun zakarun Turai wasanni 13 inda ya zura kwallo guda.

Adam Lallana wanda ya yi ta fama da raunuka a kakar wasa biyu da ta gabata ya dokawa Liverpol wasanni 126 tare da zura kwallaye 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.