Dakatarwar shekaru 2: Manchester City za ta daukaka kara
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin UEFA na dakatar da ita daga shiga gasar cin kofin zakarun Turai na tsawon kakar wasa biyu bayan samunta da laifin kashe kudin da ya wuce kima wajen sayen sabbin ‘yan wasa.
Wallafawa ranar:
Cikin wata sanarwar gaggawa da Manchester City ta fitar jim kadan bayan hukuncin UEFA na dakatar da ita daga ga shiga gasar ta zakarun Turai har tsawon shekaru 2, kungiyar ta nuna rashin jin dadi da hukuncin yayinda ta sha alwashin daukaka kara.
A cewar sanarwar ta City hukuncin na UEFA bai zo mata da mamaki ba, amma ta yi fatan samun sassauci, bayan da hukumar ta sameta da kaiwa kololuwa wajen karya ka’idar kashe kudi wajen sayen ‘yan wasa.
Karkashin hukuncin na UEFA bayan biyan tarar yuro miliyan 30 Manchester City ba kuma zata fafata a gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasa ta 2020-2021 ba da kuma 2021-2022.
A cewar sashen da ke sanya idanu kan kashe kudin kungiyoyi wajen sayen ‘yan wasa karkashin hukumar ta UEFA, Manchester City ta kashe kudaden da suka wuce ka’ida tsakan-kanin shekarun 2012 zuwa 2016 wajen sayen ‘yan wasa, haka zalika Club din ya gaza bayar da hadin kai yayin binciken UEFA.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu