Isa ga babban shafi
Wasanni

Lampard ya kosa da golan Chelsea

Bisa dukkan alamu kocin Chelsea, Frank Lampard na shirin samun sabani da mahukuntan kungiyar dangane da shirinsa na sayar da golansu, Kepa Arrizabalaga saboda rashin takuba abin kirki a baya-bayan nan.

Kepa Arrizabalaga ya kafa tarihin zama gola mafi tsada a duniya.
Kepa Arrizabalaga ya kafa tarihin zama gola mafi tsada a duniya. REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Golan mai shekaru 25 ya kafa tarihin zama mai tsaren raga mafi tsada a duniya bayan da Chelsea ta yi cefanansa akan Pam miliyan 71.6 daga Athletico Bilbao a 2018, kuma ya yi ta jan zaransa a karkashin shugabancin tsohon kocinsu, Maurizio Sarri a kakar bara.

Sai dai a baya-bayan nan karsashin dan wasan ya yi rauni, yayin da Chelsea ta ajiye shi a banci a wasanta da Leceister City a ranar Asabar bayan ta zarge shi da yin sakaci har ya bari Arsenal ta zura masa kwallaye 2 a wasan da suka yi kafin karawarsu da Leceister.

Lampard ya hakikance cewa, zai sayar da Arrizabagala a wannan kaka tare da maye gurbinsa da Nick Pope na Burley ko kuma Vicente Guaita na Crystal Palace.

Sai dai ana ganin kusoshin kuniyar ta Chelsea basa goyon bayan raba gari da Golan a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.