Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Ronaldo na iya warware matsaloli 100 a lokaci guda- Sarri

Kocin Juventus, Maurizio Sarri ya jinjina wa shahararren dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo bayan da kwallaye biyun da ya ci suka kai Juventus ga nasarar doke Parma a karshen mako.

Cristiano Ronaldo, dan wasan Juventus da Portugal
Cristiano Ronaldo, dan wasan Juventus da Portugal REUTERS/Alberto Lingria
Talla

Ronaldo ya ci kwallo daya a zubin farko na wasan, kana ya kara daya bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Zalika, dan kasar Potugal din ya bada gudummawa ainun a bangaren tsaron baya a wasan da suka fafata a Turin.

Sarri ya bayyana Ronaldo a matsayin gwarzon da ka iya ja maka matsala daya, amma kuma ya warware maka sama da matsaloli dari.

Nasarar ta Juventus kan Parma ta sa yanzu ta baiwa mai bi mata a teburin Serie A, Inter Milan ratar maki 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.