Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

FA na tuhumar De Gea da rashin da'a a wasan Manchester da Liverpool

Hukumar kwallon kafar Ingila FA na tuhumar Kungiyar Manchester United da laifin gaza baiwa ‘yan wasanta cikakkiyar tarbiyar rike fushinsu yayin wasa, bayan rashin da’ar da hukumar ta zargi mai tsaron ragar United David de Gea da aikatawa.

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United David De Gea.
Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United David De Gea. Reuters / Lee Smith Livepic
Talla

FA ta aikewa Manchester United takardar tuhuma kan yadda David de Gea ya tunkari alkalin wasa Craig Pawson a ranar lahadi bayan matakinsa na bayar da kwallon da Roberto Firmino ya zura, kwallon da daga bisani na’urar taimakwa alkalin wasa ta VAR ta soke.

A minti na 26 da fara wasan ne dai bayan mai tsaron bayan Liverpool Virgil van Dijk ya budewa Club din kwallonsu na farko kana Roberto Firmino ya zura ta biyu duk da cewa alkalin wasa ya busa usur, amma kuma alkalin yaso ya amincewa da kwallon matakin da ya harzuka ‘yan wasan na United, kafin daga bisani VAR ta soke kwallon.

Yanzu haka dai FA ta baiwa Manchester United nan da ranar Alhamis don neman gafara kana bin da ta aikata a wasan na ranar Lahadi da ta sha kaye a Anfield da kwallo 2 da nema.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.