Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

An shirya addu'o'in tunawa da Sala

Shekara guda bayan rasuwar dan kwallo Emiliano Sala, a gobe Talata za a yi addu’o’in tunawa da shi a biranen Nates da Cardiff; amma yayin da birnaen biyu suka samu hadin kai ta wajen yin makoki, mummunar hatsarin jirgin saman yana ci gaba da janyo cece – kuce.

Marigayi Emiliano Sala
Marigayi Emiliano Sala Reuters
Talla

Kungiyar kwallon kafa ta Cardiff City wacce a lokacin take wasa a gasar Firimiya ta sayi Sala daga kungiyar kwallon kafa ta Nantes kan kudi Yuro miliyan 17.

Dan wasan gaban, dan asalin Argentina yana kan hanyarsa ta zuwa sabuwar kungiyarsa ne a cikin wani karamin jirgin sama ya gamu da ajalinsa bayan jirgin ya rikito cikin mashigin ruwan Ingila.

Har yanzu babu cikakken bayani kan ummul’aba’isan wannan hatsari da ya lakume rayuwar wannan matashi dan kwallon kafa, amma ana ta gutsiri – tsoma – tsakanin ku kungiyoyin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.