Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal ta yi bikin tunawa da Kanu bayan shekaru 21

Kungiyar Arsenal ta yi bikin cika shekaru 21 da kulla yarjejeniya da tauraronta Nwankwo Kanu da ya bata gagarumar gudunmawa a gasar Premier Ingila.

Tsohon dan wasan Arsenal Nwankwo Kanu, tare da abokan wasansa Thierry Henry da Lungberg.
Tsohon dan wasan Arsenal Nwankwo Kanu, tare da abokan wasansa Thierry Henry da Lungberg. Reuters
Talla

A ranar laraba 15 ga Janairun 2020 ranar da tauraron tawagar kwallon Super Eagles ta Najeriya ya rattaba hannu kan yarjejeniya da kungiyar ta Arsenal ta zagayo.

Ranar 15 ga Janairun 1999 tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger ya kulla yarjejeniya da Kanu daga Inter Milan kan Fam miliyan 4.

A tsawon lokacin da ya shafe tare da ita kuma, Nwankwo Kanu ya bugawa Arsenal wasanni 119, inda ya ci kwallaye 44, inda ya taimaka mata wajen jin kofin gasar Premier 2, FA 2 da kuma kofin FA Comuunity Shield 1, daga bisani kuma ya koma kungiyar West Brom a shekarar 2004.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.