Isa ga babban shafi
Wasanni

Napoli ta kori Ancelotti bayan ya taimaka mata

Napoli ta kori kocinta Carlo Ancelotti kasa da sa’o’i uku da jagorantar kungiyar wajen samun nasarar tsallakawa matakin kungiyoyi 16 a gasar zakarun Turai.

Carlo Ancelotti.
Carlo Ancelotti. REUTERS/Charles Platiau/File Photo
Talla

Kungiyar wadda ke taka leda a gasar Serie A ta Italiya, ta gaza samun nasara a wasanni tara da ta buga, amma a ranar Talata ta samun nasarar doke Genk da kwallaye 4-0 a gasar zakarun Turai, abin da ya ba ta damar samun gurbin.

Kungiyar na a matsayi na bakwai a teburin gasar Serie A da maki 21, inda Inter Milan da ken jan ragamar teburin ta ba ta tazarar maki 17 .

Rahotanni na cewa, tsohon kocin AC Milan Gennaro Gattuso ne zai maye gurbin Ancelotti  a Napoli

Tuni Everton ta fara  kallon Ancelotti a matsayin babban zabinta na kocin da zai maye gurbin Marco Silva da ta raba gari da shi.

Ancelotti ya lashe kofunan zakarun Turai har guda uku a matsayin koci, daya da Real Madrid, sai kuma biyu da AC Milan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.