Zakarun Turai: Messi ya kai Barcelona zagayen kungiyoyi 16
Lionel Messi ya taimaka wa Barcelona ta samu shiga zagaye na gaba, wato na kungiyoyi 16 a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, bayan ta lallasa Borussia Dortmund 3-1 a daren Laraba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ci gaba da kasancewar Lucien Favre a matsayin kocin Dortmund na kara kasancewa cikin rashin tabbas, biyo bayan wannan dukan – kawo wuka a filin wasa Camp Nou, kuma ba kowa ne ya jefa shi cikin wannan yanayi ba illa Lionel Messi.
Dan kasar Argentina din ya ci kwallo daya, kana ya taimaka wa abokan wasan sa, Luiz Suarez da Antoine Griezmann suka ci daya kowanne, lamarin da ya ba kungiyar ta Barcelona maki 11 a rukunin F; ta ba Dortmund ratar maki 4, haka ma Inter Milan wacce ta doke Slavia Prague 3-1 har gida duk a daren Laraba.
Wannan ne kwallon Messi ta 613 a Barcelona da ya ci a wasansa na 700th a kungiyar.
Messi, ya ci kwallaye 10 a wasanni 9 da ya buga wa Barcelona a baya bayan nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu