Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

NFF na iya sallamar masu horar da tawagogin kwallon kafa na kasa a Najeriya

Akwai alamu masu karfi da ke nuni da cewa Hukumar Kwallon kafar Najeriya za ta sallami masu horar da tawagogin kwallon kafar ta na ‘yan kasa da shekaru 17, 20, 23, da ma babban tawagar kwallon kafar kasarta ‘yan wasa masu murza leda a gida, da ta mata wato, Super Falcons.

Shugaban Hukumar kwallon kafar Najeriya, Amaju Pinnick
Shugaban Hukumar kwallon kafar Najeriya, Amaju Pinnick
Talla

Kocawan da wannan al’amari ka iya rutsawa dasu dai sune: Paul Aigbogun na Flying Eagles, Christopher Danjuma na Super Falcons, wato tawagar kwallon kafar mata ta kasar, da Imama Amapakabo, mai horar da tawagar Super Eagles ta wasn masu wasa a gida, da Manu Garba na Golden Eaglets, wato tawagar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekaru 17.

Hukumar kwallon kafar kasar ta tsegunta haka ne a yayin amsa tambayoyi a takardar jan kunne da ministan wasannin kasar, Sunday Dare ya aike mata kan rashin tabuka wani abu da tawagogin da suka wakilci kasar a gasanni dabam –dabam a wannan shekarar suka yi.

Rikitowar baya – bayan nan dai ita ce wacce tawagar ‘yan wasan kasar, ta ’yan kasa da shekaru 17 ta yi a matakin kungiyoyi 16 a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Hukumar NFF ta ce ta tsara yadda za ta yi ta kaucewa rashin nasara, ta wajen yin bitar irin rawar da masu horarwa suka taka, lamarin da masu fashin baki ke ganin yana iya kaiwa ga sallama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.