Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Sada zumunta: Jamus za ta fafata da Spain, Belgium da Portugal

Kocin Jamus coach Joachim Loew ya bayyana tabbacin cewa tawagarsa za ta fafata da ta Spain a watan Maris na shekara mai zuwa, sannan ya bayyana yiwuwar haduwa da Belgium da Portugal duk a matsayin kintsawa don tinkarar gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020.

Joachim Loew babban kocin tawagar Jamus
Joachim Loew babban kocin tawagar Jamus Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Tawagar Jamus din dai ta samu gurbin fafatawa a gasar Euro bayan ta lallasa Ireland ta Arewa da ci 6-1, wasan da dan wasan Jamus din Serge Gnabry ya zuba kwallaye 3 rigis a raga.

Loew ya ce hukumar kwallon kafar Jamus na daf da tabbatar da batun wasan sada zumunta tsakanin kasar da Spain, wasan da kafafen yada labaran Spain suka ruwaito cewa a bir4nin Madrid za a gwabza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.